Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Man Shafawa Na Kashe Kwayoyin Cuta Ya Nuna Alamar Kaifi Wajen Hana Kamuwa Da Kanjamau


A yayin da akasarin masana kimiyya da dama suka dukufa kan neman hanyar warkar da cutar kanjamau ko SIDA, wasu daga cikinsu sun maida hankali ne ga samo hanyoyi mafiya nagarta na dakile yaduwar kwayar halittar dake haddasa wannan cuta, watau HIV. An dai gano cewa kororon roba yana da tasiri sosai wajen hana yaduwar wannan cuta a lokacin jima’i. Amma a wasu yankuna da dama na duniya, maza ba su so, ko kuma ba zasu iya amfani da kororon ba.

A yanzu, wani sabon bincike ya nuna cewa wani man shafawa na kashe kwayoyin cuta mai kashe kwayoyin HIV, yana iya hana mace kamuwa da wannan cuta idan ta tara da namijin dake dauke da cutar. Dr. Lameck Chinula yana aiki ma Jami’ar carolina ta Arewa a wata cibiyar da ta kafa a kasar Malawi.

Dr. Chinula ya ce, “Ana shafa wannan man kashe kwayoyin cuta a farji ko a dubura domin rage yiwuwar kamuwa da kwayar halittar cuta ta HIV mai janyo kanjamau. Wannan kuwa yana da matukar muhimmanci musamman a kasashe irinsu Malawi inda akasarin mata ba su da zabin sanya mazaje su yi amfani da kororon roba.”

Chinula yana cikin gungun wasu masana kimiyya na kasa da kasa da ake kira “Microbicide Trials Network” masu bincike kan man shafawa mai kashe kwayoyin cuta. Masu bincike a kasashe biyar sun bayar da man shafawa na kashe kwayoyin cuta ga mata su fiye da dubu uku domin su yi amfani da shi na tsawon shekara daya da rabi.

A lokacin gudanar da wannan binciken, an ba wasu matan man shafawa dake dauke da maganin kashe kwayoyin cuta, wasu an ba su man dake dauke da wani sinadari na toshe kafar shigar kwayar cutar HIV, wasu kuma an ba su man da babu wani magani a ciki amma ba tare da sun san hakan ba. Har ila yau, an ba su kororon roba, aka yi musu jinyar duk wata cutar da suke da ita wadda ake dauka ta jima’i, aka kuma sanar da su yadda zasu iya hana kawunansu kamuwa da kwayar cutar HIV.

Dr. Chinula ya ce, “Mace zata shafa wannan mai idan ta san cewar zata tara da namiji a ranar, ko kuma zata shafa ba tare da bukace shi da yayi amfani da kororon roba ba.”

Daya daga cikin abubuwan da aka gano shi ne wannan mai bai kara kasadar mace ta daukar kwayar cutar HIV kamar yadda gwajin farko da aka yi can baya da irin wannan mai ya haddasa ba. Chinula ya ce la shakka, wasu daga cikin matan da suka karbi man shafawa mai dauke da maganin kashe kwayoyin cuta sun dauki kwayar cutar ta HIV, amma yawansu bai kusanci na sauran matan da ba su shafa irin wannan mai ba.

Ya ce, “ba mu da wadatacciyar shaidar da zamu bugi kirji mu ce wannan mai yana hana mace daukar kwayar cutar HIV, amma ina da kwarin guiwar cewa shi wannan mai zai bada wata ‘yar kariya ga mata.”

Chinula ya ce wannan sakamako na binciken nasu, zai kara muhimmin bayanin da ake bukata domin gaggauta gano man shafawa na kashe kwayoyin cuta mai kaifi wanda zai zamo makamin da mata zasu iya amfani da shi nan gaba wajen kare kawunansu.

XS
SM
MD
LG