Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Rasha Biyu Da Ake Garkuwa Da Su A Niger-Delta Sun Tsere Ma 'Yan Tsageru


Rundunar sojojin Nijeriya ta ce wasu 'yan kasar Rasha su biyu da aka sace watanni biyu da suka shige, sun tsere daga hannun mutanen da suke yin garkuwa da su, kuma an ceto su.

Wani kakakin sojojin, Kanar Sagir Musa, ya ce mutanen biyu sun tsere da kafa daga sansanin da ake yin garkuwa da su. Sun shafe kwanaki biyar su na yawo a cikin fadamu na yankin Niger Delta. Jiya alhamis wasu sojojin Nijeriya dake yin sintiri a yankin suka tsince su, suka fito da su waje.

'Yan kasar ta Rasha su na yin aiki ne a wata masana'antar goran ruwa dake garin Ikot Abasi mai tashar jiragen ruwa a Jihar Akwa Ibom.

Sace mutane da kai hare-hare sun zamo ruwan dare a yankin kudancin Nijeriya mai arzikin fetur. Har yanzu Nijeriya ce kasar da ta fi sayarwa da kasashen waje man fetur a nahiyar Afirka duk da cewa yawan man da take hakowa ya ragu da kashi ashirin cikin 100 a shekaru ukun da suka shige a saboda sace-sacen mutane da hare-haren da ake kaiwa kan cibiyoyin mai na yankin.

XS
SM
MD
LG