Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yaba Da Shawarar Hambararren Shugaban Kasar Mauritaniya Ta Sasantawa A Kasar


Amurka ta yaba da shawarar da hambararren shugaban kasar Mauritaniya, Mohammed Ould Cheikh Abdellahi, ya gabatar ta maido da mulkin farar hula a kasar.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce Ould Cheikh Abdellahi ya gabatar da wannan shawara tasa ce a wurin wani taron da aka yi a birnin Paris a tsakanin jami'an Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma wakilan hambararriyar gwamnatin farar hula ta Mauritaniya.

Kakakin, Robert Wodd, ya ce shugaban na Mauritaniya ya bayar da shawarar tattaunawar da za ta kai ga maido da ikon da tsarin mulki ya ba shugaban, tare da gudanar da zabe da wuri. Har ila yau, shawarar ta Ould Cheikh Abdellahi zata ba shugabannin sojojin da suka yi juyin mulkin watan Agustar bara damar sauka salun alun daga kan mulki.

Wood yayi kira ga al'ummar Mauritaniya da sauran kasashen duniya da su rungumi wannan dama domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

A makon jiya, dubban 'yan Mauritaniya sun yi zanga-zangar rajin dimokuradiyya inda suka bukaci da a maido da Ould Cheikh Abdellahi kan gadonsa na mulki. Shi ne shugaban kasar na farko da aka zaba ba tare da ha'inci ba.

XS
SM
MD
LG