Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Ragargaza Wani bangaren Hedkwatar Rundunar Sojojin Guinea-Bissau


Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Guinea-Bissau, Janar Tagme Na Waie, ya mutu a lokacin da wani abu ya fashe a cikin hedkwatar rundunar sojojin kasar.

Wasu mutanen su biyar kuma sun ji rauni, yayin da wani bangare na hedkwatar ya lalace.

Nan da nan sojoji suka rufe gidajen rediyo masu zaman kansu a yayin da suka fara farautar wadanda suka kai harin jiya lahadi. Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Kasar Guinea-Bissau dake Afirka ta Yamma, daya daga cikin kasashen ad suka fi fama da talauci a Afirka, ta jima tana fama da tashe-tashen hankula. A cikin watan Nuwamba, wasu sojoji sun yi harbi a kan gidan shugaban kasar, Joao Bernardo Viera a wani yunkurin yi masa juyin mulki. Amma shugaban bai ji rauni ba.

XS
SM
MD
LG