Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Pakistan Ta Mika Wuya Ga Bukatun 'Yan Hamayya...


Gwamnatin Pakistan ta mika wuya ga bukatun ‘yan hamayya, ta yarda zata maido da tsohon babban jojin kasar kan kujerarsa, a wani yunkurin kawo karshen rikicin siyasa.

Madugun ‘yan hamayya, Nawaz Sharif, yayi marhabin da wannan labari, ya kuma janye macin da ya shirya yi zuwa babban birnin kasar inda dubban ‘yan raji suka shirya yin gangamin neman ‘yancin bangaren shari’a.

Firayim ministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani, shi ya bayyana wannan shawara cikin jawabin da yayi ga al’ummar kasar ta talabijin da asubahin yau litinin, a bayan da tarzomar nuna kin jinin gwamnati ta barke jiya lahadi a birnin Lahore, inda Malam Sharif yake da karfi da tasiri.

Firayim ministan yace za a rantsar da Iftikhar Mohammed Chaudry a matsayin babban jojin kasar ranar asabar, ranar da babban jojin na yanzu zai yi ritaya. Har ila yau, Firayim minista Gilani ya umurci hukumomi da su sako dukkan lauyoyi da ‘yan rajin siyasar da aka kama lokacin zanga zanga a makon da ya shige.

Daruruwan lauyoyi sun taru su na murnar wannan labari a kofar gidan Chaudry a birnin Islamabad.

XS
SM
MD
LG