Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Na Amurka Ya Sassauto Da Tarnakin Da Aka Yi Ma Kasar Cuba


Shugaba Barack Obama na Amurka ya dage tarnakin hanawa Amurkawa 'yan asalin Cuba yin tafiya zuwa kasar ko kuma aikewa da kudi ga 'yan'uwansu dake can. Wannan muhimmin sauyi ne daga tsauraran manufofin da gwamnatin shugaba George Bush ta dauka kan tsibirin mai bin tafarkin kwaminisanci.

Jiya litinin fadar White House ta ce shugaba Obama ya umurci sakatariyar harkokin waje da sakatarorin Baitulmali da Kasuwanci da su dauki matakan da suka kamata na janye wannan tarnaki. Kakakin fadar ta White Houuse, Robert Gibbs, ya ce Mr. Obama ya bada umurnin daukar wasu jerin matakai na mika hannun abota ga al'ummar Cuba domin tallafawa muradunsu na samun muhimman 'yancin walwala. Amma Gibbs ya ce tilas ne ita ma kasar Cuba ta dauki wasu matakan.

Daya daga cikin matakan da aka bada sanarwar dauka jiya litinin zai kyale kamfanonin sadarwa na Amurka su nemi lasisin samar da wayoyin salula da kuma telebijin ga al'ummar tsibirin. Wani matakin kuma ya fadada irin kayayyakin da aka yarda a aika da su zuwa Cuba ciki har da sutura da iri na shuka, da kayan kamun kifi da wasu kayan na bukatar yau da kullum.

Shawarar dai ba ta dage takunkumin cinikayyar da aka kafa ma Cuba shekaru 47 da suka shige ba.

XS
SM
MD
LG