Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon lafiya Ta Duniya Ta Ce Murar Aladu Ta Zamo Annoba


Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta kara tsananin gargadin da ta bayar game da annobar murar aladu da ta barke, abinda ke nufin cewa a yanzu wannan cuta tana yaduwa tsakanin jama'a tun daga matakin unguwanni.

Litinin jami'an Hukumar WHO suka bayyana kara tsananin gargadin da suka bayar daga mataki na 3 zuwa na 4, watau saura matakai biyu a ayyana wannan cuta a zaman annoba mai barazana ga illahirin bil Adama. Wannan shawara ta kara tsananin gargadin ta biyo bayan rahotannin da aka samu cewar cutar ta kashe mutane 149, ta kwantar da wasu mutane dubu daya da dari shida a kasar Mexico.

Hukumar WHO ta dauki wannan matakin a daidai lokacin da sakatariyar Tsaron Cikin Gida ta Amurka, Janet Napolitano, ta ce Amurka tana daukar matakai tamkar barkewar wannan cuta ta murar aladu ta zamo cikakkiyar annoba, kuma za a ci gaba da yin aiki da kashedin da ake yi wa jama'a na gujewa zuwa kasar Mexico muddin aka ci gaba da ganin wannan cuta a can.

Sakatariya Napolitano ta fadawa 'yan jarida a nan Washington cewa tana tuntubar jami'ai a kasar Mexico domin tsara irin matakan da za a dauka game da wannan cuta da ta barke.

Mexico ta rufe dukkan makarantu a fadin kasar har sai mako mai zuwa, ta kuma umurci jama'a da su ringa sanya mayani ko wani abinda zai rufe musu hanci da baki a wani yunkurin dakile yaduwar cutar.

An tabbatar da cewa mutane arba'in sun kamu da cutar a nan Amurka, yayin da aka samuw asu mutane shida da ita a kasar Canada. Litinin kasar Spain ta tabbatar da mutum na farko dake dauke da kwayar cutar a kasarta, yayin da ake binciken wasu da ake kyautata zaton sun kamu da ita a kasashen New Zealand, Faransa, Isra'ila da kuma Scotland. Wasu daga cikin masu fama da laulayin sun koma kasashensu ke nan daga ziyara zuwa kasar Mexico.

XS
SM
MD
LG