Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman Bincike Na Kasashe Da Dama Su Na Neman Jirgin Fasinja Da Ya Bace Dauke Da Mutane 228


Jirage na kasashe da dama su na ci gaba da bincike a yau talata ko zasu gano jirgin saman fasinja na kamfanin Air France wanda ya bace jiya litinin lokacin hadari a tekun Atlantika. Jiragen saman bincike na kasashen Faransa da Brazil da Spain su na bin sawu ko zasu gano abinda ya faru ga wannan jirgi kirar Airbus A330, wanda ya tashi zuwa Paris daga birnin Rio de Janeiro dauke da mutane 228.

Su na bincike wani yankin teku mai fadin murabba’in kilomita dubu daya a arewa maso gabas da gabar jerin tsibiran Fernando de Noronha na kasar Brazil. Jiragen sama dauke da na’urorin bincike na musamman sun shafe tsawon dare su na bin sawun jirgin da ya bata.

Haka kuma, Brazil ta tura jiragen ruwan soja zuwa wurin da ake zaton jirgin saman fasinjar na Air france ya fado, amma kuma ba zasu isa wurin ba sai daren yau talata ko kuma safiyar gobe laraba.

Jami’an kamfanin safarar jiragen saman Brazil na TAM sun ce daya daga cikin matuka jiragensu ya ce ya ga alamun wuta tana ci cikin teku a lokacin da yake wucewa ta sama a daidai inbda ake kyautata zaton jirgin na Air France ya fadi.

XS
SM
MD
LG