Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Kasar Gabon Sun Tabbatar Da Mutuwar Shugaba Omar Bongo


Shugaban da ya fi kowa jimawa kan kujerar shugabancin wata kasa a nahiyar Afirka, shugaba Umar Bongo na Gabon, ya rasu a wani asibitin kasar Spain. Firayim minista Jean Eyeghe Ndong, yace Mr. Bongo, mai shekaru 73 da haihuwa, ya rasu a bayan da ya gamu da murdewar zuciya.

Jim kadan a bayan da aka bada sanarwar mutuwar Mr. Bongo a Libreville babban birnin kasar, an rufe bakin iyakokin kasar ta sama da kasa da kuma teku, sannan aka killace muhimman gine-gine.

Ma’aikatar tsaron Gabon, wadda ke karkashin jagorancin dan marigayin, Ali Ben Bongo, ta ce an sanya dukkan dakarun tsaron kasar cikin damarar ko ta kwana, jami’ai kuma sun yi kiran da a kwantar da hankula.

Za a yi zaman makoki na tsawon kwanaki 30 a Gabon domin tuna Bongo, wanda yayi shekaru fiye da arba’in da daya yana mulkin wannan kasa dake tsakiyar Afirka. Tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugabar majalisar dokoki, Rose Francine Rogombe, zata shugabanci gwamnatin rikon kwarya tare da shirya sabon zaben shugaban kasa.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan Umar Bongo da al’ummar kasar Gabon, ya kuma yaba da rawar da marigayin ya taka wajen habaka dangantakar Amurka da gabon.

XS
SM
MD
LG