Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gini Ya Rushe Ya Kashe Mutane Akalla Biyar A Lagos


Hukumomin Nijeriya sun ce mutane akalla biyar sun mutu a lokacin da wani gini mai hawa uku ya rushe a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar. An ceto wasu mutanen su akalla talatin.

Masu aikin ceto sun ce haka kwatsam wannan gini ya rushe ranar lahadi. Babu wani bayanin da aka samu a game da dalilin rushewar wannan bene.

A watan Maris, mutane akalla 11 sun mutu a lokacin da wani benen mai hawa hudu shi ma ya rushe a birnin na Lagos.

Rushewar gine-gine dai ba sabon abu ba ne a Nijeriya, inda magina suke yin ko oho da ka'idojin yin gini da gwamnati ke shimfidawa, suke kuma yin amfani da kayayyakin ginin da ba su dace ba, ko kuma ba su da aminci.

XS
SM
MD
LG