Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Hambarar Da Shugaban Honduras Mai Shirin Yin Tazarce


Mutumin da 'yan majalisar dokokin Honduras suka nada a matsayin shugaban kasa na riko, a bayan da aka hambarar da shugaba Manuel Zelaya, ya ce ya hau kan wannan kujera ta hanyar halal.

Roberto Michelleti, shugaban majalisar dokokin Honduras, ya fada jim kadan a bayanda aka rantsar da shi cewa hambarar da Mr. Zelaya da aka yi ba juyin mulki ba ne. Ya kuma kafa dokar hana yawon dare har zuwa ranar talata.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki-moon, da jami'an gwamnatin Amurka sun yi tur da cire Mr. Zelaya da aka yi daga kan karagar mulki. Amurka ta ce ba zata amince da wata gwamnati a Honduras ba im ba ta Mr. Zelaya ba. Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ce babban Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya zai yi zaman gaggawa lyau litinin domin tattauna wannan batun.

Lahadi ne sojojin Honduras suka kama Mr. Zelaya, sannan suka tura shi kasar Costa Rica da sanyin safiyar wannan rana da ya kebe domin gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan tsarin mulki domin ba shi damar yin tazarce.

A lokacin da yake magana daga Costa Rica, Mr. Zelaya ya ce sace shi aka yi, kuma ba zai yarda da duk wata gwamnatin da zata maye gurbin ta sa ba. Yayi alkwarin sai ya gama wa'adinsa a kan mulki.

XS
SM
MD
LG