Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mamadou Tandja Ta Ce Lallai Sai Ta Gudanar Da Kuri'ar Raba-Gardama


Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce za a gudanar da kuri'ar raba-gardamar da zata iya ba shugaba Mamadou Tandja damar yin tazarce, duk da cewa kotu ta haramta yin hakan, 'yan hamayya kuma sun nuna rashin yardarsu.

A lokacin da yake magana lahadi, ministan harkokin cikin gidan Nijar, Albade Abouba, ya ce lallai za a gudanar da wannan kuri'ar raba-gardama, har ma ya nuna yatsar yin barazana ga 'yan hamayya dake kushe shugaba Tandja.

A ranar jumma'a shugaba Tandja ya ce daga yanzu zai rungumi ragamar mulki a kasar shi kadai, a bayan da Kotun Tsarin Mulki ta Jamhuriyar Nijar ta jaddada hukumcin da ya haramta gudanar da kuri'ar raba-gardama domin sauya tsarin mulki.

A ranar asabar, 'yan hamayya na Nijar sun bayyana matakan da shugaba Tandja ya dauka a matsayin juyin mulki, sun kuma yi kira ga dakarun tsaron kasar da su ki bin umurnin da shugaban zai ba su.

Shugaba Tandja da 'yan kanzagin Tazarce su na son a gudanar da kuri'ar raba-gardamar a ranar 4 ga watan Agusta.

XS
SM
MD
LG