Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Hana Jirgin Shugaba Manuel Zelaya Na Honduras Sauka A Tegucigalpa


Hambararren shugaban kasar Honduras, Manuel Zelaya, ya sauka a San Salvador, babban birnin kasar El Salvador, domin ganawa da sauran shugabannin kasashen yankin Latin Amurka, a bayan da sojoji suka hana jirginsa sauka a kasarsa da maraicen lahadi. A bayan da ya kasa sauka a Tegucigalpa, hambararren shugaban ya yada zango na wani dan lokaci a kasar Nicaragua.

A nan San salvador, Mr. Zelaya zai gana da shugabannin kasashen Argentina, Ecuador da kuma Paraguay. Haka nan zai gana da sakatare-janar na Kungiyar Kasashen Amurka.

Shugaba Zelaya ya fadawa gidan telebijin na Telesur da maraicen lahadi cewa sojoji sun toshe hanyar saukar jirage a filin jirgin saman Tegucigalpa, suka hana ma jirgin nasa sauka. Hambararren shugaban ya ce zai yi kokarin sake komawa Honduras nan gaba kadan.

A halin da ake ciki, gwamnatin rikon kwaryar Honduras ta kafa dokar hana fita har zuwa asubahi a bayan da aka kashe wani dan zanga-zanga guda a filin jirgin saman. Dubban 'yan zanga-zanga suka fito lahadi, daga baya gangamin nasu ya rikide ya koma yamutsi.

A bayan mutum guda da aka kashe, mutane da dama sun ji rauni a arangamar da aka yi a tsakanin dakarun tsaro da dubban magoya bayan Mr. Zelaya.

XS
SM
MD
LG