Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Ahuwa Ga Tsageran Niger-Delta Yana Tafiyar Hawainiya A Nijeriya


Da alamun shirin da gwamnatin Nijeriya ta bullo da shi na yin ahuwa ga ‘yan tsagera a yankin Niger Delta mai arzikin man fetutr yana tafiyar hawainiya.

Tun lokacin da aka fara aiwatar da shirin na kwanaki 60 makonni biyu da suka shige, daruruwan ‘yan tsagera sun mika makamansu. Wannan adadin kuwa, kalilan ne daga kiyasin cewa yawan ‘yan tsagera dake dauke da makamai zai kai dubu 10.

An ce da yawa daga cikin ‘yan tsageran su na dari-darin mika makamansu saboda fargabar cewa gwamnati ba zata cika alkawarinta na yin ahuwar ba. Jami’an Nijeriya su na fata tsagera masu yawa zasu mika makamansu a karshen makon nan.

A watan Yuni shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Nijeriya yayi tayin ahuwa ga tsageran da suka daina kai hari kan cibiyoyin mai suka ajiye makamansu nan da ranar 4 ga watan Oktoba.

XS
SM
MD
LG