Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Tarurruka A Fadin Duniya Don Tunawa Da Hare-Haren 11 Ga Watan Satumba


Sojojin Amurka kimanin dubu daya a kasar Afghanistan sun tuna da ranar kai hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba ta hanyar gudanar da tseren kilomita 10.

Sojojin dake sansanin mayakan sama na Bagram, sun sanya takalmansu na gudu domin tuna wannan rana shekaru 8 da suak wuce, lokacin da aka kashe mutane kusan dubu uku a hare-haren ta'addanci a kan Amurka.

A halin da ake ciki, shugabannin kasashen duniya su na bayyana bakin ciki tare da nuna goyon bayansu. Firayim minista Vladimir Putin na Rasha ya ce kasarsa tana jimamin mutanen da aka kashe ranar 11 ga watan Satumba. Kamfanin dillancin labarai an Itar-Tass, ya ambaci Mr. Putin yana fadin cewa wannan rana, manuniya ce ag dukkan kasashe cewar ya kamata su ajiye sabaninsu a gefe guda, su yaki abokin gabansu su duka, watau ta'addanci.

A Kyrgyzstan, shugaba Kurmanbek Bakiyev, ya lura da gwagwarmayar da kasarsa ta jima tana yi da ta'addanci da kuma shirinta na yaka ta'addanci a ko da yaushe.

Mr. Bakiyev yayi magana ne a filin jirgin saman Manas, dake wajen Bishkek, inda Amurka ta ke da wata babbar cibiyar zirga-zirgar jiragen saman dake kai kayan bukatu ma sojojin dake kasar Afghanistan.

XS
SM
MD
LG