Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsageran Taliban Sun Kai Farmaki Kan Wasu Sansanoni Biyu Na Sojojin Amurka Dake Cikin Lungu


Hukumomin Afghanistan sun ce daruruwan tsagera sun kai farmaki a kan wasu sansanoni biyu na sojojin Amurka dake cikin lungu sosai a lardin Nuristan na arewa maso gabashin kasar, a kusa da bakin iyaka da Pakistan, suka kashe sojojin Amurka 8 da na Afghanistan 2.

Wata sanarwar rundunar sojojin Amurka ta ce kazamin fada ya barke tun da asubahin asabar a gundumar Kamdesh, a bayan da wasu 'ysan tsagera na yankin dauke da makamai masu yawa suka kaddamar da wani irin farmaki mai sarkakiya.

Wani kakakin rundunar sojojin Amurka, ya shaidawa Muryar Amurka cewa jiya lahadi cewa an shafe kusan tsawon asabar ana dauki-ba-dadi. Kanar Wayne Shanks yace sojojin kawance sun yi amfani da dukkan makaman da zasu iya, ciki har da jiragen helkwafta na kai farmaki, domin fatattakar maharan, tare da kashe 'yan tsagna masu yawa.

Yace sojojin dake yankin sun samu nasarar hana tsageran kama wadannan sansanoni, kuma su na sintiri a yankin yanzu domin hana sake kai wani farmakin.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan farmakin, ta kuma ce ta kama 'yan sandan Afghanistan da dama tana rike da su. Jami'an Afghanistan sun ce wasu daga cikin tsageran sun fito ne daga Pakistan.

Lamarin tsaro ya kara tabarbarewa a Afghanistan tun farkon shekarar nan. Kwamandan sojojin Amurka a can, Janar Stanley McChrystal, ya bukaci karin sojoji domin fuskantar abinda ya kira lamari mai kamari.

Amma a wata hirar da aka yi da shi jiya lahadi, mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jim Jones, yace Afghanistan ba ta cikin kasadar fadawa hannun 'yan Taliban. Yace lamarin na Afghanistan yana da sarkakiya, kuma ba za a iya warware shi ta hanyar tura karin sojoji kawai ba. Yace tilas a samu ci gaba a fagagen tsaro da bunkasar tattalin arziki da mulki na kwarai duk a lokaci guda.

XS
SM
MD
LG