Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Zata Kyale Sufetoci Su Binciki Masana'antar Nukiliyarta Dake Qom Ranar 25 Ga Watan Oktoba


Babban jami’in nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yace Iran zata kyale sufetoci su ziyarci sabuwar masana’antar nukiliyarta da aka gano a kusa da Qom, ranar 25 ga watan Oktoba.

Mohammed el-Baradei ya bayyana wannan jiya lahadi, bayan da ya gana da jami’an Iran a birnin Teheran.

A lokacin wannan tattaunawa kuma, Iran ta yarda zata sake ganawa da manyan kasashe 6 na duniya ranar 19 ga watan nan na Oktoba a birnin Geneva.A lokacin da sassan suka gana ranar alhamis da ta shige a birnin Geneva, Iran ta yarda zata kyale a binciki masana’antar ta Qom.

El-Baradei ya fada jiya lahadi cewa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA, ba ta da kwakkwarar shaidar cewa Iran tana da wani shirin kera makamai. Amma yace har yanzu hukumar tana nazarin zarge-zargen cewa Iran ta nazarci makaman nukiliya.

Jakadiyar Amurka a MDD, Susan Rice, ta ce akwai rahotanni dabam-dabam, kuma duk sun sha bambam, a kan ko Iran ta mallaki fasahar kera makaman nukiliya. Ta ce idan Iran ba ta yi watsi da shirin da ake zargin tana da shi na makaman nukiliya ba, zata fuskanci karin takunkumi.

Iran dai ta ce shirin nukilirta na zaman lumana ne.

XS
SM
MD
LG