Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Zaben Ali Ben Bongo


Kotun tsarin mulki ta Gabon ta tabbatar da nasarar da Ali Ben Bongo ya samu a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Agusta. Litinin kotun kolin ta Gabon ta yi watsi da dukkan zarge-zargen da 'yan hamayya suka yi na gagarumin magudi lokacin wannan zaben.

Hukumcin kotun ya biyo bayan umurnin da ta bayar na sake kidaya dukkan kuri'un da aka kada a zaben, kidayar da aka kammala a makon da ya shige.

Sakamakon da hukuma ta bayar ya ba Mr. Bongo kashi 42 cikin 100 na kuri'un da aka jefa.

'Yan takara guda tara na jam'iyyun hamayya sun kalubalanci sakamakon. 'Yan takarar sun hada da Mba Obame da Pierre Mamboundou, wadanda suka zo na biyu da na uku, a bayan da kowannensu ya samu kimanin kashi 25 daga cikin 100 na kuri'un da aka jefa.

Akasarin 'yan kallon zabe sun ce an kamanta gaskiya, duk da samun magudin da bai taka kara ya karya ba.

Ali Ben Bongo, da ne ga marigayi Omar Bongo, wanda ya shafe shekaru fiye da arba'in yana mulkin kasar Gabon akfin rasuwarsa a watan Yuni.

XS
SM
MD
LG