Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Fara Ziyararsa Ta Farko A Nahiyar Asiya


Shugaba Barack Obama na Amurka yana kan hanyarsa ta zuwa Tokyo a kasar Japan, a bayan da yayi jawabi ga sojojin Amurka a wani sansanin mayakan sama dake birnin Anchorage a Jihar Alaska, jihar da ta fi girma kuma ta ke kuryar arewacin Amurka.

Mr. Obama ya fadawa sojoji a sansanin mayakan sama na Elmendorf cewar ba zai ja kafa ba wajen yin amfani da karfi domin kare Amurka da muradunta, amma kuma ba zai jefa rayukan sojoji cikin hatsari ba sai idan hakan ya zamo dole. Yace Amurka zata goyi bayan sojojinta a kasashen waje, da kuma iyalansu a nan gida.

Haka kuma ya lura cewa da yake yanzu ya ziyarci Jihar Alaska, ke nan ya ziyarci dukkan jihohi hamsin na Amurka.

Shugaba Obama ya fadawa ‘yan jarida kafin ya bar nan Washington cewa zai tattauna da shugabannin duniya a kan yadda za a kara bude kasuwannin kasashen Asiya da na yankin tekun Pacific ga kayayyakin da Amurka take sarrafawa.

XS
SM
MD
LG