Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Switzerland Ta Doke Nijeriya A Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Samari


Ta dai leko, amma sai ta koma ga miliyoyin 'yan Nijeriya da suka sa rai tare da nuna kwadayin lashe kofin duniya na samari 'yan kasa da shekara 17 da aka kammala a Nijeriya lahadin nan.

'Yan Nijeriya su kimanin dubu sittin suka cika babban filin wasa na kasa dake Abuja, babban birnin kasar, amma kash, sai samarin kasar Switzerland suka ba kowa mamaki, suka doke 'yan Golden Eaglets na Nijeriya da ci daya mai ban haushi, suka fita filin wasan da kofin duniya na samari 'yan kasa da shekara 17.

Dan wasan Switzerland mai suna Haris Seferovic, shi ne ya jefa kwallo kwaya daya tak a wannan arangama a cikin minti na 63 da fara wasa, lokacin da ya sa kai ya daki kwallon cikin raga.

Wannan shi ne karon farko da Switzerland ta samu shiga gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta samari 'yan kasa da shekara 17. Kai, wannan ma shi ne karon farko da kasar Switzerland ta taba lashe wata gasa da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta shirya.

Nijeriya ce kasar da ta fara lashe wannan gasa ta 'yan kasa da shekara 17 a lokacin da aka fara gudanar da ita a 1985 a kasar Sin (China). Ita ce kuma ta ke rike da kofin kafin 'yan Switzerland su amshe.

Samarin kasar Spain sun zo na uku a bayan da suka doke takwarorinsu na Colombia da ci daya mai ban haushi.

Sai dai Samarin Nijeriya ba su tafi hannu banza ba. An zabi dan wasan Nijeriya, Sani Emmanuel, a zaman zakara na wannan gasa baki dayanta. Emmanuel ya jefa kwallaye har guda biyar a lokacin wannan gasa, duk kuwa da cewa sai daga baya ake sanya shi cikin wasa.

Bakin ciki a Nijeriya dai yau kam, kusan gidan kowa da shi.

XS
SM
MD
LG