Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama


Jami'an sojan kasar Iran sun ce sun fara gudanar da wata gagarumar rawar-daji ta kare kai daga hare-hare ta sama, wadda ta zo daidai lokacin da Iran ta ke kara shan matsin lamba daga waje kan shirinta na nukiliya.

Jami'ai suka ce wannan rawar-daji ta hada da gwajin kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin nukiliya na iran a wani bangare na kare msana'antun daga hare-hare.

Kafofin labarai na kasar Iran sun fada jiya lahadi cewa za a shafe kwanaki biyar ana gudanar da wannan rawar-daji wadda za a yi ta a cikin yanki mai fadin murabba'in kilomita dubu dari shida a yankunan tsakiya da yammaci da kuma kudancin Iran.

Amurka da Isra'ila har yanzu ba su ce ba za su dauki matakan soja a kan Iran ba idan har aka kasa warware batun nukiliya na Iran ta hanyar diflomasiyya.

Shugaban mayakan sama na rundunar juyin juya halin Iran, Amir Ali Hajizadeh, ya ce idan har jiragen saman kai farmaki na bani Isra'ila suka samu kubucewa fannonin tsaron samaniyar Iran, to sojojin kasar za su far ma sansanonin Isra'ila da makamai masu linzami da ake cilllawa daga doron kasa zuwa doron kasa.

A lokacin da yake magana jiya lahadi a birnin al-Qahira, shugaban bani Isra'ila, Shimon Peres, ya ce Isra'ila ba ta yin barazana ga kowa. Ya ce kasarsa tana yin adawa ne da shugabannin kasar Iran na yanzu, ba wai tana yi ne da al'ummar Iran ba.

XS
SM
MD
LG