Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Zai Bayyana Sabuwar Manufarsa Kan Afghanistan A Ranar Talata


Fadar White House ta ce shugaba Barack Obama zai bayyana sabuwar manufarsa kan Afghanistan ranar talata da daddare, a cikin wani jawabin da zai yi ga kasa daga babbar makarantar horas da sojoji ta Amurka dake West Point a Jihar New York.

Jiya laraba kakakin fadar ta White House, Robert Gibbs, ya bada sanarwar shirin na shugaba Obama. Gibbs yace sojojin Amurka sun shafe shekaru takwas yanzu haka a kasar Afghanistan, ya kuma ce Amurka ba zata zauna a can Afghanistan na wasu karin shekaru 8 ko 9 ba.

Wannan sanarwa ta biyo bayan makonnin da shugaban ya shafe yana ganawa da manyan masu ba shi shawara game da tsaron kasa a kan hanyoyin da suka kamata a bi don takalar batun Afghanistan.

Kafofin labarai sun ba da rahotannin cewa a bisa dukkan alamu, Mr. Obama zai amince da wani shirin da ya tanadi tura karin sojoji akalla dubu 30 na Amurka zuwa can. Mr. Obama ya lashi takobin karasa aikin da aka fara a Afghanistan. A yanzu haka akwai sojojin Amurka dubu 68 a Afghanistan din.


XS
SM
MD
LG