Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kidaya Kuri'u A Zaben Shugaban Kasar Da Ake Gardama Kai A Kasar Honduras


Kuri'un neman ra'ayoyin masu jefa kuri'a na farko sun nuna cewa wani dan takarar jam'iyyar hamayya ne yake kan gaba a zaben shugaban kasa na lahadi da ake gardama kai a Honduras, zaben da aka shirya da nufin kawo karshen rikicin siyasar watanni biyar a kasar.

Kafofin labarai na Honduras sun bayar da rahoton cewa dan ra'ayin rikau, Porfirio "Pepe" Lobo, yana kan gaba da fiye da kashi hamsin cikin dari na kuri'un. Rahotannin suka ce ya ba da rata ma Elvin Santos na jam'iyyar Liberal kuma tsohon mataimakin shugaba na hambararren shugaban kasa Manuel Zelaya.

Jami'an zabe sun yaba da yadda aka gudanar da wannan zabe ba tare da tangarda ba, da kuma yawan masu jefa kuri'ar da suka fito lahadi, duk da arangamar da aka yi a birnin San Pedro Sula a arewacin kasar. 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin su tarwatsa 'yan zanga-zanga masu goyon bayan Mr. Zelaya, wanda yayi kiran da a kauracewa zaben.

Babu daya daga cikin Mr. Zelaya ko Roberto Micheletti, shugaban da sojoji suka dora kan mulki, da ya shiga yayi takara a cikin wannan zaben.

Amurka da Costa Rica da kuma Peru sun ce watakila za su amince da sakamakon zaben na lahadi, matakin da zai sa su yi sabani da kasashen Latin Amurka, cikinsu har da Brazil da Venezuela da kuma Argentina, wadanda suka ce ba za su yarda da sakamakon zaben ba.

XS
SM
MD
LG