Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tana Shirin Gina Sabbin Masana'antun Tace Makamashin Uranium


Gwamnatin Iran ta ce tana shirye-shiryen gina sabbin masana'antun tace makamashin Uranium guda goma, masu kama da babbar masana'antar tace Uranium dinta dake Natanz.

Kafofin labarai na hukumomin kasar sun ce tuni har an amince da wasu wurare biyar don kafa sabbin masana'antun, yayin da aka umurci Hukumar Makamshin Nukiliya ta Iran da ta samo wasu karin wurare biyar.

Babban jami'in nukiliya na kasar Iran, Ali Akbar Salehi, ya ce za a gina sabbin masana'antun a karkashin duwatsu domin kare su daga hare-hare, kuma zasu yi amfani da sabbin butoci mafiya nagarta wajen tace karfen na Uranium don maida shi makamashi.

Wannan sanarwa ta gwamnatin Iran game da fadada shirinta na nukiliya da ake gardma a kai, ta zo a daidai lokacin da manyan kasashen duniya da kuma Hukumar Nukiliya ta Duniya suek kokarin dakile ayyukan kasar na tace makamashin Uranium.

Kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, Robert Gibbs, ya ce Iran zata keta alkawuran duniya da suka rataya a wuyarta idan ta yi hakan. Ya kara da cewa wannan wani karin misali ne na yadda Iran ta ke zabin mayar da kanta saniyar ware.

Britaniya ta bayyana sanarwar ta Iran a zaman babbar abar damuwa, yayin da Jamus ta bukaci hukumomi a birnin Teheran da su cika alkawuran da suka yi ma duniya.

XS
SM
MD
LG