Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Ta Ce 'Yan Sandan Nijeriya Su Na Kashe Daruruwan Fararen Hula A Kowace Shekara


Kungiyar "Amnesty International" ta ce 'yan sanda a Nijeriya su na kashe daruruwan fararen hula da mutanen da suke zargin masu aikata laifi ne, ta hanyoyin da suka saba da dokokin kasa.

A cikin wani rahoton da ta wallafa larabar nan, kungiyar kare hakkin bil adamar mai hedkwata a London, ta zargi 'yan sandan Nijeriya da laifin mummunan keta hakkin bil adama, ciki har da kashe mutane ba tare da gurfanar da su a gaban kotu da samunsu da laifi ba, da ganawa mutane azaba da kuma batar da wasu mutanen.

Rahoton ya ce an kashe 'yan fashi da makami dari takwas da hamsin da bakwai, aka ji rauni ma wasu guda hamsin da uku a shekarar 2008.

Jami'a mai kula da ayyukan kungiyar ta Amnesty a Nijeriya, Lucy Freeman, ta ce kashe 'yan fashi ba tare da kai su gaban kotu ba, ya zamo kamar wani karbabben abu, kuma 'yan sanda suka wallafa labaran kashe 'yan fashin domin su nuna wa jama'a cewa su na yin aiki tukuru.

Kungiyar kare hakkin bil adamar ta yi kira ga 'yan sandan Nijeriya da su yi amfani da karfin da zai iya kaiwa ga mutuwa wajen kare rayuka kawai.

Kakakin rundunar 'yan sandan Nijeriya, Manuel Ojukwu, ya bayyana wannan rahoto na Amnesty a zaman gurguntacce, yana mai cewa rahoton bai ambaci daruruwan 'yan sandan da su ma ake kashewa wajen gudanar da ayyukansu a kowace shekara ba. Ya ce ana gudanar da bincike a duk lokacin da dan sanda ya kashe wani.

XS
SM
MD
LG