Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutane Kimanin Casa'in A Nijeriya


Rahotanni daga Nijeriya sun ce mutane akalla casa'in (90) sun mutu a lokacin da wata babbar mota ta kwace ta abka cikin mutane a wata kasuwa dake cike da mutane lokacin.

An ce akalla mutane arba'in (40) sun ji rauni a wannan hatsarin da ya faru asabar a yankin karamar hukumar Dekina, a Jihar Kogi dake tsakiyar kasar.

Jami'an Nijeriya sun ce wannan barbbar mota ta kwace ma direbanta, ta kara da wasu motocin, sannan ta bi ta kan wasu mutane dake kusa da nan.

Jami'an gwamnatin tarayyar Nijeriya sun ce mutane hamsin da biyar (55) suka mutu, amma 'yan jarida a wurin da abin ya faru sun ce mutane akalla casa'in (90) ne suka mutu.

An saba ganin munanan hadarurruka na motoci a Nijeriya inda hanyoyi ke cike da ramuka, yayin da direbobi kuma ba su bin dokokin hanya, su na yawaita gudu na ganganci.

XS
SM
MD
LG