Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Indiya Sun Ce Mutanen Da Suka Mutu A Rushewar Wata Sabuwar Gada Da Ake Ginawa Zai Kai Arba'in


Jami’an Indiya sun ce watakila mutane akalla 40 ne suka mutu a lokacin da wata gada ta rushe a yankin yammacin kasar. Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Rajasthan, ya fada yau asabar cewa har yanzu akwai gawarwaki da yawa a cikin kogin Chambal a kusa da garin Kota.

Jami’ai suka ce wannan gada da ta rushe ranar alhamis da maraice, ana aikin gina ta ne, kuma har an kaddamar da binciken musabbabin rushewarta.

An tura sojoji wadanda suka wkare wajen iyo domin su tallafa wajen cetowa tare da samo gawarwakin mutane daga cikin kogin.

XS
SM
MD
LG