Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Nemi Karin Hadin Kai Da Kasashen Musulmi Wajen Inganta Tsaron Jiragen FasinjaShugaba Barack Obama a jawabin nasa na daren jiya Alhamis yace Gwamnatinsa Amurka zata yi aiki wajen tabbatarda kasa aiki da bayanan sirri, da gazawar matakan tsaro da suka kai ga yunkurin harin ta'addanci cikin wani jirgin fasinja bai sake faruwa ba.An kuma sami ci gaba a bincken da ake yi. Yace an fara samun nasarar karya lagon shugabannin al-qaida, ana kuma binsu ana kashesu, Amurka na samun cikakken hadin kai daga kawayenta, cikinsu harda kasar Yemen, wadda yanzu haka ke sahun gaban masu daukan matakan ruguza akidar shugabannin al-qaida, domin Amurka ta sami nasarar janyo cikas wajen hanasu aiwatar da shirinsu na kaiwa Amurka harin ta'addanci a ciki da wajen Amurka.

Shugaba Obama ya kara da cewa, Amurka ta sani mafi yawan Musulmi da kasashen Musulmin kasa da kasa basa baiwa al-qaida goyon baya. Wannan ya nuna ke nan al-qaida idonta ya rufe wajen neman inda zata rika daukan sojin hayarta da zata horas domin yi mata ayyukanta na ta';addanci, alqaida tafi maida hankali yanzu a yankin gabas na tsakiya, dawasu sassa na Afirka. Wannan shine dalilin da yasa shugaba Obama ya baiwa jami'an tsaron Amurka umarnin zaunawa domin gano sabbain hanyar daza'a bi wajen cin dungumin ayyukan al-qaida ta kowace hanya.

Ya kuma zama wajibi Amurka ta rungumi Musulmin kasa da kasa wajen musayar bayanai domin bambancewa da akidar Islama da ayyukan ta'addanci. Shugaba Barack Obama yace duk da cewar ba wanda za'a azawa laifi ko wata ma'aikatar Gwamnatin dake da laifin kin gudanar da ayyukansu, amma ba daidai bane a sami wagegen gibin abinda ya bada damar yin barazanar.

Kuma yace wajibi ne a kansa a matsayinsa na shugaban Amurka ya dauki duk matakin da ya dace domin kare lafiyar Amerkawa. Shugaba Barack Obama yana mai cewa shi kam baya sha'awar nuna yatsa ko aza laifi a kan wani ko wata, shi muhimmin abinda yafi damuwa dashi shine, gano hanyar bi domin gyara kuskuren da aka yi domin hana sake afkuwar kuskuren tare da daukan matakan karfafa kare lafiyar Amerkawa da tsaron Amurka.

Shugaba Barack Obama, ya yi jawabi ne a daren jiya Alhamis bayan yayi tilawar rahoton binciken sakacin jami'an Gwamnatin da ya afku game da daukan matakan tsaron kasa, sannan shugaban ya tattauna sakamakon rahoton da babban jami'in dake bashi shawara kan harkokin tsaro. Shugaba Obama ya girgiza kai tare da yin nadamar abinda ya afku:

Dan Nigeria, Umar Faruk Abdulmatallab, ya sami shiga jirgin saman fasinjan Amurka ne daga tashar jirgin saman Amsterdam a ranar Kirsimeti, lokacin ne kuma yayi kokarin tada bom din da ya kunshe shi a jikin bantensa. Kuma tun farko saida mahaifinsa ya shaidawa jami'an hukumomin Amurka halin da dansa ke ciki na cusa kansa a rikicin da ba zai iya daukan nauyinsa ba.

Babban jami'in dake baiwa shugaban Amurka shawara kan gano hanyar dakile ayyukan ta'addanci John Brennan, yace a zahiri ba wani ma'aikacain Gwamnatin Amurka da za'a azawa laifin kin aiki da rahoton asirin da aka bayar game da shirin tada bom a jirgin saman, amma sun gaza aiki da bayanai da suka samu wajen kan Umar Faruk har suka kyaleshi ya shiga jirgin saman da ya kawo shi Amurka, inda matsalar take ke nan. John Brennan ya kara da cewa, jami'an ayyukan cin dungumin ta'addanci a Amurka sun gano cewar ana kokarin shirya kai harin ta'addancin, amma abinda basu gano ba shine a wace ce kuma wane lokaci, a dai dailokacin da ake wnanan tunanin ne kuma 'yan ta'addar ke kokarin tura Umar Mutallab zuwa Amurka.

XS
SM
MD
LG