Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Togo Zasu Koma Gida


An janye kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Togo daga Angola, a bayan wani mummunan harin da aka kai kan motar kungiyar har aka kashe mutane uku.

Tun fari kuwa, 'yan wasan na kasar Togo sun bayyana kwadayin ci gaba da zama tare da shiga gasar ta cin Kofin Kwallon Kafar Kasashen Afirka da ake farawa yau a kasar ta Angola. Amma ‘yan wasan sun fadawa ‘yan jarida yau lahadi cewa gwamnatin Togo tana son su koma gida, kuma zasu bin wannan umurni nata.

A ranar jumma’a, an kai farmaki a kan motar ‘yan wasan Togo a lokacin da suke tsallakawa daga cikin Kwango ta Kinshasa zuwa cikin yankin Cabinda na Angola. ‘Yan bindiga sun kashe direban motar, da mataimakin mai koyar da wasa na ‘yan Togo da kuma kakakin kungiyar.

Wasu mutanen su akalla 7 sun ji rauni. Cikinsu har da mai tsaron gida na ‘yan wasan Togo, Kodjovi Obilale wanda aka dauka zuwa Afirka ta Kudu, aka yi masa tiyata. An ce yana murmurewa a can yanzu haka

XS
SM
MD
LG