Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOJOJIN NAJERIYA NA KOKARIN KASHE WUTAR RIKICIN DA YA BARKE A JOS, JAHAR FILATO


Sojojin Najeriya na kokarin shan kan tarzoma a birnin Jos da kewaye bayan barkewar fada tsakanin Kirista da Musulmi a ranar lahadi.

Shaidu sun ce da yammacin jiya talata fadan ya bazu zuwa wasu sabbin unguwanni bayan da mataimaikin shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bada umarnin tura sojoji zuwa garin Jos sannan kuma hukumomi su ka fara karfafa dokar hana fita dare da rana.

Jami’an gwamnatin Najeriya sun ce mutane 27 aka kashe a cikin tashin hankalin, amma shugabannin Musulmi da na Kiristoci da kuma ma’aikatan ceton gaggawa sun ce yawan mace-macen ya dara haka, su ka ce mutane 150 zuwa 300 ne su ka mutu. Amma ba a tabbatar da gaskiyar wannan adadi ba.

Kungiyar ayyukan agajin jin kai da taimakon gajiyayyu ta Red Cross ko Croix Rouge ta kiyasta cewa mutane dubu biyu a kalla sun rasa matsuguni.

Har yanzu babu tabbas game da mafarin tashin hankalin. Da halama dai ya na da nasaba da gina wani Masallaci.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bada umarnin tura sojoji cikin garin Jos a lokacin da shugaba Umaru Musa ‘Yaradua ba ya kasar, wanda watanni kusan biyu kenan ya na kwance a wani asibitin kasar Saudiyya ya na jinya.

XS
SM
MD
LG