Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Najeriya ta bada wa'adin tabbatar da lafiyar shugaba Yar'adua.


Wata kotun tarayya a Najeriya taba majalisar zartaswar kasar wa'adin kwanaki goma sha hudu ta yanke hukumci kan ko shugaba Umaru Yar'adua yana iya ci gaba da shugabancin kasar. Kotun ta yanke hukunci yau jumma'a cewa tilas ne majalisar ta tsaida shawara kan makomar 'Yar'adua kafin cikar wa'adin. Babban lauyan gwamnati janar Micheal Aondoakaa ya ci alwashin kiyaye hukumcin tare da tsaida shawara dangane da rashin lafiyar shugaba Yar'adu'a kamar yadda kotun ta umarta.Shugaba Yar'adua ya bar Najeriya ne watanni biyu da suka shige domin jinyar ciwon zuciya a kasar Saudiya. Shugaban kasar dan shekaru 58 ya kuma yi fama da ciwon koda. Kotun ta yanke hukunci ne bisa karar da aka shigar cewa Mr. Yar'adua ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa da ya ki mika mulki a hukumance ga mataimakinsa Goodluck Jonathan kamar yadda doka ta tanada. Makon jiya wata kotun Najeriya ta yanke hukumci cewa Goodluck Jonathan yana iya gudanar da ayyukan shugaban kasa ba tare da mika mashi mulki a hukumance ba.

XS
SM
MD
LG