Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Hamayya A Jamhuriyar Nijar Sun Yi Zanga-Zanga A Birnin Yamai


Dubban 'yan hamayya da suka yi zanga-zanga jiya lahadi a Jamhuriyar Nijar sun zargi shugaba Mamadou Tandja da laifin kanainaye mulki tare da gurgunta shawarwarin da ake yi da nufin warware rikicin siyasar kasar.

Shugabannin gamayyar jam'iyyun hamayya da kungiyoyin kwadagon Jamhuriyar Nijar da ake kira "CFDR" a takaice, sun yi jawabi gaban gangamin na jiya lahadi a Yamai, babban birnin kasar. Suka ce Mr. Tandja shi ne ummul-haba'isin wargajewar shawarwarin da kungiyar ECOWAS ko CDEAO ta ke gudanarwa.

A makon da ya shige, kungiyar ta gamayyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta dakatar da shawarwarin a bayan da sassan biyu na jamhuriyar Nijar suka kasa cimma daidaituwa kan wani daftarin yarjejeniya wadda mai shiga tsakani, kuma tsohon shugaban Nijeriya, Abdulsalami Abubakar, ya gabatar ga sassan.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa yace yarjejeniyar da aka nemi sassan su amince da ita zata kyale Mr. Tandja ya ci gaba da mulki na rikon kwarya na wani kayyadadden lokaci. Har ila yau ta tanadi cewa a nada firayim minista daga bangaren 'yan hamayya, a yi garambawul ga tsarin mulki, sannan a gudanar da sabon babban zabe na kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG