Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Goce Da Harbe-Harbe Kusa Da Gidan Shugaba Mamadou Tandja


An goce da harbe-harben bindigogi a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, a dab da fadar shugaban kasar a wani abinda jami'an gwamnati ke bayyanawa a zaman yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja.

Shaidu sun bayar da labarin barkewar harbe-harbe da manyan bindigogi har da mashin gan babu kaukautawa yau alhamis da tsakar rana a birnin na Yamai. An girka sojoji cikin damara a a kusa da fadar shugaban kasar, yayin da jama'a suka watse daga titunan dake kusa da nan.

Wasu majiyoyin gwamnati sun fadawa Sashen Hausa cewar an dauki wasu da suka ji rauni zuwa asibiti.

Ba a dai san ko su wanene ke da hannu a harbe-harben ba, amma jami'an gwamnatin shugaba Tandja su na bayyana wannan lamarin a zaman yunkurin juyin mulki.

Tankiya ta karu a kasar da ke Afirka ta yamma cikin 'yan watannin nan a bayan da shugaba Mamadou Tandja ya kara tsawon wa'adinsa kan mulki fiye da yadda tsarin mulki ya tanada. A farkon makon nan, dubban 'yan hamayya sun yi gangami a Yamai domin bayyana rashin jin dadinsu da rikicin siyasar da ake fama da shi.

Wa'adin Mr. Tandja a kan mulki ya kare a karshen watan Disambar bara, amma a cikin w atan Agusta ya gudanar da kuri'ar raba gardama domin sauya tsarin mulkin kasar tare da ba kansa karin shekaru uku a kan karagar mulki.

A lokacin da majalisar dokokin Nijar da kuma kotun tsarin mulki ta kasar suka bayyana cewar kuri'ar raba gardamar da ya shirya ta haramun ce, sai shugaban ya rushe dukkan cibiyoyin biyu ya amshe dukkan bangarorin mulkin kasar. A ranar da abin ya faru, Amurka ta dakatar da duk wani agaji wanda ba na jinkai ba da take ba Nijar ta kuma kafa takunkumin tafiye tafiye a kan jami'an gwamnatin Mr. Tandja.

XS
SM
MD
LG