Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kama Shugaba Mamadou Tandja


Rahotanni da dumi-duminsu daga Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar, sun ce sojoji sun abka cikin fadar shugaban kasar, sun kuma kama shugaba Mamadou Tandja sun tafi da shi wani wuri.

Shaidu sun bayar da rahoton jin kararrakin harbe-harbe yau alhamis da tsakar rana a kewayen fadar shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambaci wani direba a fadar shugaban dake fadin cewa sojojin sun abka cikin fadar shugaban a lokacin da ake gudanar da taron ministoci. Wani dan jarida a birnin ya ce sojojin sun fita da shugaba Tandja, kuma ba a san inda yake a yanzu ba.

An ga sojoji a kusa da fadar shugaban kasar, kuma jama'a sun watse daga titunan dake kusa da nan.

Ba a san ko su wanene ke da hannu a wannan lamarin ba.

XS
SM
MD
LG