Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Hambarar Da Mamadou Tandja Daga Kan Mulki


Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar kafa sabuwar Babbar Majalisar Maido da Dimokuradiyya, a bayan da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja.

A cikin wata sanarwar da kakakin sabuwar majalisar da ake kira "CSRD" a takaice cikin harshen Faransanci, Kanar Abdoulkarim Goukoye, ya bayar ga 'yan jarida, yace an dakatar da yin aiki da tsarin mulki, yayin da aka rushe dukkan cibiyoyin da aka kafa karkashin tsarin mulkin.

Sojojin sun yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, su na masu fadin cewa ba su yi juyin mulkin domin kuntatawa wani ko wasu ba.

Sabbin hukumomin kasar ta Nijar sun bayyana kafa dokar hana fita waje daga karfe shida na maraice zuwa shida na safe.

Babu wani karin hasken da kakakin na sojoji ya bayar a game da halin da Mamadou Tandja yake ciki, haka kuma babu wani bayani game da ministocinsa da aka ce an kama su.

XS
SM
MD
LG