Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya Ta Janye Jakadanta Daga Mali


Aljeriya ta janye jakadanta dake kasar Mali a yau talata, domin ta nuna rashin jin dadin yadda hukumomin Mali suka saki wasu tsagera hudu masu kishin Islama domin tsageran su sako wani Bafaranshe da suka kama su na yin garkuwa da shi.

Kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida a Yankin Maghreb ta kama wani Bafaranshe mai suna Pierre Camatte a kasar Mali, ta kuma yi barazanar cewa zata kashe shi idan har hukumomi ba su sako wadannan mutane hudu zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu. An saki tsageran hudu ranar lahadi, amma har yanzu ba a ji ko yaushe ne za a sako Bafaranshen, ko ma za a sako shi din ba.

A yau talata ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fito da kakkausar harshe tana yin Allah wadarai da abinda ta kira "halin rashin abota" na kasar Mali.

Ita ma kasar Mauritaniya ta janye jakadanta dake kasar Mali jiya litinin domin nuna bacin ran wannan abu da hukumomin Mali suka yi. Daga cikin tsageran da aka sake akwai wani dan kasar Mauritaniya da ake nema ruwa a jallo, bisa tuhumar aikata ta'addanci.

Aljeriya tana neman biyu daga cikin tsageran 'yan kasarta domin ta gurfanar ad su gaban shari'a, ita ma bisa tuhumar ta'addanci.

XS
SM
MD
LG