Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Da 'Yan Tawayen Darfur Sun Cimma Tsagaita Wuta


Gwamnatin Sudan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar 'yan tawaye mafi girma da tasiri a yankin Darfur, a wani bangare na alkwarin kawo karshen yakin shekaru 7 a yankin.

Cikin daren talatar nan shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar da Kungiyar Adalci Da Daidaito, JEM, a wani buki a daular Qatar.

Wannan yarjejeniya bangare ce ta alkwarin da Sudan da Chadi suka yi kwanakin baya na kawo karshen zaman gaba a bakin iyakar kasashensu. Kowaccensu tana zargin makwabciyarta da laifin goyon bayan 'yan tawayen makwabtan.

A wani bangare na wannan yarjejeniya, Sudan ta yarda zata ba 'yan tawayen mukaman gwamnati, zata soke hukumcin kisan da aka yanke a kansu, sannan zata sako kashi 30 cikin 100 na 'yan tawayen dake daure a kurkuku.

Rikicin yankin darfur ya hallaka mutane dubu 300, yayin da wasu kimanin miliyan biyu da dubu 700 suka rasa matsuguni.

XS
SM
MD
LG