Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Sace Maaikatan Tashar Talabijin Supersport Ta Afirka Ta Kudu


Yan bindiga a Najeriya sun kai hari kan wata motar safa dake dauke da ma’aikatan gidan talabijin na SuperSport suka sace mutane uku jiya Litinin.

Rahotanni daga Lagos sun nuna cewa, yan bindigan sun yi garkuwa da ‘yan Najeriya guda biyu da kuma wani dan Afrika ta kudu daya. A kalla daya daga cikin mutanen, dan asalin Afrika ta kudu dan jarida ne ma’aikacin tashar SuperSport aiki. Tashar talibijin din ta Afrika ta kudu tace ba a gabatar mata wata bukatar kudin fansa ba, sai dai zata tura wani babban jami’in kamfanin zuwa birnin Ikko domin neman sanin abinda ya faru.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an gwamnatin Afrika ta kudu da kuma kamfanin SuperSports suna shirin fitar da sanarwai yau Talata.

XS
SM
MD
LG