Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zabe Wakilan Majalisar Dokokin Iraqi Yau Lahadi


An bude rumfunan zabe ako ina a duk fadin Iraqi domin zaben wakilan majalisar dokokin kasar.

Ana kallon wan nan zabe a matsayin zakarar gwajin dafin karfin kasar na tabbatarda doka da oda,kuma ta mika iko cikin lumana,bayan harin mayaye da Amurka ta kaiwa kasar a 2003.Kusan ‘yan ksar dake da ikon zabe kamar milyan ashirin ne za su zabi wakilan majalisa 325 cikin ‘yan takara dubu shida.Za’a cigaba da zabe har zuwa karfe biyar na yammma agogon Bgadaza.

An zafafa matakan tsaro da dubun dubatan sojojin Iraqi da ‘Yansanda suna sintiri kan tituna don hana yi yuwar akai hari. ‘Yansanda sunce an yi harbi da bindigogin egwa da yawa kan wasu rumfunan zabe a Bagadaza dab da bude wuraren zaben.Babu wani rahoto nan take na wata jikkata mai tsanani.

Jiya Asabar,wani bam da ka nasa cikin wata mota ya tashi kan wasu motoci biyu na ‘yan yawon bude ido a birnin Najaf,ya kashe mutane hudu, ya jikkata fiyeda mutane hamsin.

Wata kungiya mai alaka da al-Qaida dake kiran kanta Iraqi mai bin tafarkin Islama, ta yi gargadin cewa duk wadda ya fita jefa kuri’a to zai fuskanci kisa.

An karfafa matakan tsaro a biranen Iraqi,da ma akan iyakokinta da Iran da Syria, gabannin zaben na ranar lahadi.

XS
SM
MD
LG