Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kararrakin Harbe-Harbe Sun Firgita Mutane Talata A Kusa Da Jos


Mazauna yankin tsakiyar Nijeriya sun ce sun ji kararrakin harbe-harbe a kusa da wasu kauyukan da aka hallaka daruruwan mutane cikinsu a farkon makon nan. Shaidu a wannan wuri dake kusa da Jos sun ce kararrakin harbe-harben sun sa mutane sun sheka kan tituna su na neman mafaka jiya talata da maraice.

Ba a dai san ko wani ya ji rauni ba, haka kuma ba a fahimci ko su wanene suke harbe-harben ba.

A ranar litinin, jami'ai sun jagoranci binne mutane a kauyen Dogo Na Hauwa, daya daga cikin kauyukan da akasarin mazaunansa Kiristoci ne a kusa da Jos, wadanda makiyaya Musulmi suka kai ma farmaki ranar lahadi.

Wani jami'in gwamnatin Jihar Filato, Solomon Zang, yace an binne mutane kimanin 380. Amma har yanzu ba a san zahirin ko mutane nawa suka mutu a wannan tashin hankali ba.

A bayan wannan kashe-kashen, gwamnatin Amurka, ta roki al'ummar Nijeriya da su kai zuciya nesa. P.J. Crowley, shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, kuma ya bada sanarwa yana cewa, "Muna bayyana tsananin takaicinmu da ci gaba da tashin hankali da kuma hasarar rayuka a garin Jos. Muna kira ga dukkan sassan da abin ya shafa, da su kai zuciya nesa, su kuma samu hanyoyi masu ma'ana na takalar batun zub da jinin da ya ki ci ya ki cinyewa a Jihar Filato. Haka kuma muna son mu ga gwamnatin tarayyar Nijeriya Nijeriya ta tabbatar da cewa ta hukumta mutanen da suke haddasa wannan zub da jinin."

Shi ma jakadan Britaniya a Nijeriya, Bob Dewar, yace wannan sabon tashin hankalin da aka yi a Jos ya sake nuna irin bukatar dake akwai ga gwamnatin Nijeriya kan ta dauki kwararan matakan kawo karshen wadannan kashe-kashe na babu gaira babu dalili. A lokacin da yake bayyana jajensa ga mutanen da abin ya shafa, Mr. Dewar yace Britaniya zata yi marhabin da duk wani matakin da Nijeriya zata dauka na kwantar da wutar wannan lamari da hana shi yaduwa. Mr. Dewar yace su na rokon dukkan sassan da su nemi hanyoyin lumana na warware matsalolinsu, ciki har da tattaunawa tsakanin mabiya addinai dabam-dabam.

XS
SM
MD
LG