Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Didier Drogba Shi Ne Zakaran Kwallon Kafa Na Afirka Na 2009


An zabi dan wasan kwallon kafa dan asalin kasar Cote D’Ivoire, Didier Drogba, a zaman zakaran wasan kwallon kafa na nahiyar Afirka a shekarar 2009.

Jiya alhamis Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka, CAF, ta mika wannan kambi ga dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila, wanda shi ne karo na biyu da yake zama zakaran kwallon kafa na nahiyar.

A baya, Drogba ya zamo zakara a shekarar 2006.

Samuel Eto’o dan kasar Kamaru shi ne ya zo na biyu a lokacin wannan zabe da masu koyar da wasannin kasashen dake cikin hukumar CAF suke jefawa. Michael Essien dan kasar Ghana, kuma dan wasan kungiyar Chelsea ta Ingila, shi ne ya zo na uku.


XS
SM
MD
LG