Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zirga Zirga Tsakanin Arewa Da Kudancin Najeriya Ta Tsaya Cik Ranar Jummaa


Zirga zirga tsakanin arewaci da kudancin Najeriya ta tsaya cik a yinin jumma’a sakamakon zanga zangar masu tuka manyan motoci dake dakon kaya, da abinci zuwa kudu.Suna zanga zangar ce kan zargi da suke yi cewa jami’ai a jihohin Kwara,Oyo,Ogun da Ondo,da ma wasu zauna gari-banza, suna matsa musu da karbar haraji na babu gaira babu dalili.

Wakilinmu na Legas, Ladan Ibrahim Ayawa,wadda zanga zangar ta rutsa da shi a Jebba, yace mutane da suka samu a hayin gadan, sun ce tun takwas na safe suke wurin. Lokacin da ya yi magana da Washington, da misalin karfe goma na dare yace bai san lokacin da zasu bar wurin. Masu zanga zangar wadanda tun farko suke hana manyan motoci masu dakon kaya,sai suka shiga hana masu kananan motoci ma ma wucewa. Tsahon motoci ya kai kilomita 15.

XS
SM
MD
LG