Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta dauki Alhakin Hare Hare Da Ya Kashe Akalla Mutane Talatin a Kandahar


Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wani jerin hare-haren boma-bomai da ya girgiza birnin Kandahar jiya Asabar,ya kashe akalla mutane 30.

Wani dan uwan shugaba Hammed karzai, yace maharan sun kai hari ne kan cibiyoyi hudu a birnin,amma babbar fashewa ta aukune a kofar babbar fursina dake birnin. Ahmed Wali Karzai,wadda shine shugaban lardin Kandahar ya ce jami’ai sun hakikance burin harin na jiya Asabar shine yunkurin sako fursinoni. Wani irin wan nan haria 2008 ya baiwa daruruwan fursinoni damar tserewa ciki harda wadanda ake zargi cewa ‘yan kungiyar Taliban su 400.

Rahotanni akafofin yada labarai sunce,wata sanarwaa yanar gizon Taliban tace harin sako ne ga kungiyar tsaro ta NATO.A farkon makon jiya babban kwamandan mayakan AmurkaaAfghanistan,Janar Stanley McChrystal yace burinsana gaba shine sake kwace Kandahar,babbar tungar Taliban.

XS
SM
MD
LG