Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Faransawan Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Darfur


Faransa ta ce an sako wasu ma’aikatan agaji su biyu da aka kama kusan watanni hudu da suka shige daga yankin Darfur na kasar Sudan. Ministan harkokin wajen Faransa, Bernard Kouchner, ya fada cikin wata sanarwa cewar an sako ‘yan aikin agajin biyu jiya lahadi kuma sun doshi Khartoum, babban birnin Sudan.

Mutanen biyu, Olivier Denis da Olivier Frappe, sun yi magana da ‘yan jarida a bayan da likitoci suka duba lafiyarsu. Denis yace ba a musguna musu ba, kuma sun ci sa’a da yake su biyu ne.

An sace mutanen biyu ma’aikatan kungiyar agajin kasar Faransa mai suna "Triangle" ranar 22 ga watan Nuwamba a garin Birao na kasar Afirka ta Tsakiya. Wannan garin yana bakin iyakar kasar da kasashen Sudan da Chadi.

Wata kungiyar dake kiran kanta "Freedom Eagles of Africa" ta dauki alhakin sace mutanen biyu da kuma wani ma’aikacin agaji na uku dan kasar Faransa a gabashin Chadi. A watan da ya shige aka sako daya ma’aikacin mai suna Laurent Maurice.

XS
SM
MD
LG