Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Sabon Rikici A Jihar Filato


<!-- IMAGE -->

An kashe mutane akalla 13 a tashin hankali na baya-bayan nan a kusa da garin jos dake tsakiyar Nijeriya.

Shaidu sun ce mahara sun kai farmaki kan wani kauye mai suna Byei wanda akasarin mutanensa Kiristoci ne a kudu da Jos, suka cunna wuta a gidaje suka kai farmaki kan mutane da adduna a yayin da suke fitowa da gudu.

Mazauna kauyen suka ce maharan sun batar da sawu suka yi shiga kamar sojoji. Jami'an gwamnati a yankin sun dora laifin wannan harin a kan Fulani makiyaya wadanda akasarinsu Musulmi ne.

An bayar da rahoton bacewar mutane akalla biyu, yayin da aka dauki mutane da dama da suka ji rauni zuwa wani asibiti.

Garin Jos da kewayensa ya sha fama da irin wannan tashin hankali, a wani bangare a saboda gasar ko wanene zai mallaki filayen gonaki masu albarka dake wannan wuri.

An kashe mutane fiye da 200, akasarinsu Kiristoci, a wani harin da aka kai kan kauyuka uku dake kudu da Jos a watan nan. A cikin watan Janairu kuma, an kashe mutane fiye da 300, akasarinsu Musulmi a tashin hankali a cikin Jos da kewaye.

XS
SM
MD
LG