Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Goodluck Jonathan Ya Mika Sunayen Wasu Ministocinsa Ga Majalisar Dattijai


Goodluck Jonathan Ya Mika Sunayen Wasu Ministocinsa Ga Majalisar Dattijai

<!-- IMAGE -->

Mai rikon mukamin shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana wasu daga cikin ministocinsa, a bayan da ya rushe majalisar ministocin kasar a makon da ya shige. Jiya laraba, shugaban majalisar dattijan Nijeriya, David Mark, ya karanta sunayen mutane 33 da shugaban ya gabatar ga majalisa ba tare da ya bayyana ma’aikatun da ake son tura su ba.

A yanzu dai, majalisar zata yi zaman tace mutanen da aka gabatar.

Sunayen da Mr. Jonathan ya gabatar sun hada da mutane 9 daga cikin ministocin da aka sauke a makon jiya, cikinsu har da daya daga cikin manyan magoya bayansa, tsohuwar ministar yada labarai Dora Akunyili.

Sabbin fuskoki cikin sabuwar majalisar ministocin sun hada da Alhaji Murtala ‘Yar’aduwa, dan marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa, wan shugaba Umaru ‘Yar’aduwa.

A rubuce dai har yanzu shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa shi ne shugaban Nijeriya, amma tun lokacin da ya kwanta jinya a watan Nuwambar bara, har yau jama’a ba su sanya shi a idanunsu ba. Makonni shida da suka shige majalisar dokokin Nijeriya ta ayyana mataimakin shugaba Goodluck Jonathan a zaman shugaban riko.

A makon jiya Mr. Jonathan ya rushe majalisar ministocin kasar a wani matakin jaddada ikonsa, da kuma abinda ya kira sanya sabbin jini cikin gwamnati. Amma wani mai fashin bakin siyasa a Abuja, Idris Aliyu, ya fadawa VOA cewa jerin sunayen da aka mika bai cimma wannan gurin sanya sabbin jinin ba, domin kuwa ya kunshi sunaye da yawa daga tsohuwar majalisar ministocin kasar.

Ana sa ran nan bada jimawa ba Mr. Jonathan zai tura karin sunayen ministoci ga majalisar dattijan. Tsohuwar majalisar ministocin dai tana da wakilai 42 ne. Jami’ai sun ce ranar litinin majalisar dattijan zata fara duba sunayen mutanen.

XS
SM
MD
LG