Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama-Bamai Sun Tashi A Birnin Moscow Yau Litinin


Bama-Bamai Sun Tashi A Birnin Moscow Yau Litinin

<!-- IMAGE -->

Kafofin labarai na Rasha sun ce mutane akalla 34 sun mutu a sanadin wasu fashe-fashe biyu da suka abku a jiragen karkashin kasa na birnin Moscow lokacin da ake ribibin zuwa aiki da safe yau litinin. Wasu mutanen su 10 sun ji rauni a fashewar farko a tashar Lubyanka yau da safe.

Tashar tana kusa da hedkwatar hukumar tsaro ta tarayya ta Rasha, watau hukumar leken asirin kasar.

Rahotannin sun ce mutane har 14 suka mutu cikin jirgin, wasu da dama suka mutu a dandalin cikin tashar ta Lubyanka.

Kamfanonin dillancin labarai na Rasha sun ce minti talatin bayan fashewar farko, an yi ta biyu a wata tashar mai suna Park Kultury. Babu wani bayanin da aka samu nan take na abinda ya haddasa fashe-fashen, amma wasu rahotanni sun fara cewa hare-haren bam ne.


XS
SM
MD
LG