Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Amurka Sun Gurfanadda Mutane Tara Mayakan Sakan Wata Kungiyar  Kirista Gaban Kotu


<!-- IMAGE -->

Hukumomin shara’a anan Amurka,sunce an tuhumci wasu mutane tara ‘yan wata rundunar kishin addinin kirista da laifin kulla makircin kashe wani dansanda da kuma shirya kai hari a lokacin wata jana’iza da fatar kashe karin ma’aikatan tsaron.

Wannan sanarwar da aka bada jiya ta biyo ne bayan rahottanin da aka bada na kama mutane takwas a jihohin Indiana, Michigan da Ohio, wadanda kuma suka hada dashi jagoran kungiyar kirstocin mai suna David Brian Stone, matarsa da ‘yayansa biyu maza.

Jiya da marece ne ma aka cafke daya daga cikin ‘yayan, Joshua Stone, 21, a gidansu dake Michigan. Takardun tuhumar sunce wannan kungiyar kiristocin dake kiran kanta Hutaree, ta na da akidar daura yaki ne da Amurka, kuma ta shirya kai hare-hare da dama daga cikin watan Afrilun nan da za’a shiga.

XS
SM
MD
LG