Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kasa Da Kasa Zata Fara Sauraron Kara Kan Rikici Da Ta Biyo Bayan Zabe A Kenya


Kotun Kasa Da Kasa Zata Fara Sauraron Kara Kan Rikici Da Ta Biyo Bayan Zabe A Kenya

Babban mai gabatar da kara na Kotun kasa da kasa dake hukunta masu aikata manyan laifuffuka ya ce ofishinsa na shirin fara sauraren akalla shari’o’I biyu masu alaka da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da a ka gudanar a Kenya a 2008.’

Mr Luis Moreno-Ocampo ya kira taron yan jarida a birnin Hague, yau Alhamis, kwana guda bayan da alkalan Kotun suka amince a fara binciken tashin hankalin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,300.

Moreno-Ocampo ya ce binciken zai fi maida hankali kana bin da ya kira,”wadanda suka fi daka rawa a laifuffuka mafiya muni.” Bai ambaci sunan kowa ba amman ya ce da alamar za a tuhumi daga mutum daya zuwa biyu kan akalla zarge-zarge iri biyu.

XS
SM
MD
LG