Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Fitaccen Dan Siyasa A Sudan Ya Janye Daga Takara A Zaben Kasar Mai Zuwa


Wani Fitaccen Dan Siyasa A Sudan Ya Janye Daga Takara A Zaben Kasar Mai Zuwa

Jami’ai a Kudancin Sudan sunce wani shahararren dan takarar Shugaban kasa a zaben da ke tafe ya fice daga takarar. Jami’an wata tsohuwar Kungiyar Yan tawayen kasar,na kungiyar The Sudan People’s Liberation Movenent, sun ce dan takararsu Mr Yasir Arman, ya janye daga takarar.

Mr Arman da shuwagabannin jama’iyyar sun ce janyewar ta Arman ta zama tilas saboda matakan shirya magudi da kuma ci gaban tashe-tashen hankula a yankin Darfur.

Ada dai ana ganin Arman a matsayi wadanda za su yi kare jinni biri jinni da Shugaba Omar Al-Bashir, a babban zaben kasar wanda za a fara ran 11 ga wannan wata na Afrilu.

XS
SM
MD
LG